Kaneem Today

Header
collapse
...
Home / Hausa / Labaru / An Gudanar da Addu’ar Al-Qunut Domin Samun Zaman Lafiya a Jihohin Arewa

An Gudanar da Addu’ar Al-Qunut Domin Samun Zaman Lafiya a Jihohin Arewa

2026-03-13  MOHAMMED YAKUBU LAILAI  21 views

Daga Mohammed Yakubu Lailai, Potiskum

An gudanar da addu’ar Al-Qunut ta musamman domin neman zaman lafiya da kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke addabar wasu jihohin Arewacin Najeriya, a Masallacin Sarkin Fika da ke garin Potiskum, Jihar Yobe.

Addu’ar wadda ta gudana a ranar Juma’a ta samu halartar manyan malamai, shugabannin al’umma da dimbin jama’ar musulmi, inda aka roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya kawo ƙarshen hare-haren da ake fuskanta a jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina, Kebbi, Yobe da Borno, tare da sauran yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Arewacin ƙasar.

Malaman da suka jagoranci addu’ar sun jaddada muhimmancin komawa ga Allah a lokutan ƙalubale, suna mai kira ga al’umma da su ƙara haƙuri, addu’a da haɗin kai domin shawo kan matsalolin da suke fuskanta.

A cikin addu’ar, an kuma roƙi Allah ya kare rayuka da dukiyoyin al’umma, ya ba shugabanni hikima da adalci wajen tafiyar da al’amuran mulki, tare da taimaka musu wajen kawo ƙarshen ayyukan ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da sauran masu tayar da zaune tsaye a yankin.

Masallacin Sarkin Fika da ke Potiskum dai na daga cikin manyan cibiyoyin ibada a yankin, inda ake gudanar da tarukan addini da addu’o’i a lokuta daban-daban domin neman zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana fatan cewa irin wadannan addu’o’i za su taimaka wajen rage matsalolin tsaro da ke addabar al’umma, tare da jawo hankalin jama’a da shugabanni kan muhimmancin haɗin kai wajen samar da zaman lafiya mai dorewa.

Rahotanni sun nuna cewa matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren ‘yan bindiga da kungiyoyin ‘yan ta’adda na ci gaba da jefa al’ummomin wasu jihohin Arewacin Najeriya cikin fargaba, lamarin da ke kara bukatar addu’a, hadin kai da matakan tsaro daga hukumomi.

Addu’ar Al-Qunut dai na daga cikin addu’o’in da Musulmi ke yi musamman a lokutan fitina ko musibu, domin neman taimakon Allah da kariyarsa ga al’umma.


Share: